Wasu dalibai daga ƙaramar hukumar birnin Kano da ke karatu a jami’ar Northwest Kano, na fuskantar barazanar rasa gurbin karatunsu, sakamakon zargin da suka yi na gazawar samun tallafin biyan kuɗin makaranta daga wajen yan siyasar yankin da suka yi musu da alƙawarin tallafi.
Daliban sun bayyana cewa, duk da tabbacin da suka samu daga ɗan majalisar tarayya na yankin, Hon. Sagir Ƙoƙi, akan zai tallafawa karatun su amma daga baya sun gaza samun taimakon, sannan suka ce basu samu ƙarin bayani ba bayan tuntubar su.
A cewar ɗaliban, sun nemi taimako daga wajen yan siyasa da dama sai dai babu wanda ya iya share hawayen su har kawo wannan lokaci.
Jami’ar ta bayyana ranar Lahadi 24 ga watan Agusta, a matsayin wa’adin ƙarshe na karɓar kuɗaɗen makaranta, abin da ya ƙara tayar da hankalin ɗaliban, musamman ganin cewa mafi yawansu mata ne masu ƙaramin ƙarfi.
Ƙungiyar ɗaliban ta roƙi gwamnatin Jihar Kano da masu hannu da shuni da su kawo musu ɗauki cikin gaggawa, inda suka ce rashin samun taimakon na iya zama babban koma baya ga makomar rayuwar su.