Ban ce dole sai na zama shugaban ƙasa ba–Atiku

0
16

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana cewa burinsa shi ne ganin Najeriya ta samu ci gaba mai ɗorewa, tsaro da ingantaccen shugabanci.

Atiku ya bayyana haka ne yayin wani taron tabbatar da sababbin masu sauya sheka zuwa jam’iyyar ADC a Legas, inda aka karɓi wasu manyan ‘yan siyasa daga PDP da LP.

Atiku, wanda Farfesa Ola Olateju na jami’ar Achievers, Owo, ya wakilta, ya ce

“Manufar Atiku ita ce samar da ingantacciyar Najeriya. Ba wai sai shi ya zama shugaban kasa ta kowanne hali ba, abin da muke so shi ne gwamnatin da za ta yi wa ‘yan kasa aiki. ADC ba kawai jam’iyya bace, motsi ne na al’umma don samar da sabuwar Najeriya.”

Daga cikin wadanda suka sauya sheka zuwa ADC akwai Dr. Abimbola Ogunkelu, tsoffin shugabannin PDP a Legas Chief Muritala Ashorobi da Capt. Tunji Shelle, da sauran manyan jiga-jigan PDP.

An karɓe su ne daga manyan shugabannin ADC na kasa, ciki har da Ogbeni Rauf Aregbesola da Sen. Kolawole Ogunwale.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here