
Shugaban Rundunar Tsaro ta Najeriya (CDS), Janar Christopher Musa, ya danganta yawaitar kashe-kashe da hare-hare a sassan kasar nan akan gabatowar zaben shekarar 2027.
Najeriya na fuskantar sake yawaitar hare-haren ta’addanci a Arewa maso Gabas da kuma na ‘yan bindiga a Arewa maso Yamma, inda jihohin Benue da Filato suka ci gaba da kasancewa cibiyoyin rikice-rikice. A ranar Litinin da ta gabata, akalla mutum 34 aka kashe a wani masallaci da ke Unguwar Mantau a karamar hukumar Malumfashi, jihar Katsina.
Janar Musa, yayin da yake magana a shirin Politics Today na tashar talabijin ta Channels a daren Alhamis, ya bayyana cewa karuwar matsalar tsaro a bana na da alaka da harkokin siyasa da ke gabatowa.
’Yan ta’adda da ‘yan bindiga suna aiki tare saboda burinsu daya ne su tarwatsa al’umma kuma su tara kudi. Amma akwai hannun ƴan siyasa a ciki. Wasu mutane ba sa son zaman lafiya saboda idan an samu zaman lafiya, gwamnati na samun yabo. Idan babu zaman lafiya, gwamnati na fuskantar suka. Bara mun samu raguwar mace-mace, amma me ya sa yanzu komai ya karu? Zabe na tafe, kuma ba za a yi watsi da yiwuwar cewa wasu na daukar nauyin wadannan miyagun ayyuka ba. Amma abin takaici, ta yaya za ka kashe mutanen da kake son mulkarsu?” in ji shi.
Ya ce har yanzu akwai masu daukar nauyin ta’addanci daga cikin gida da waje, inda ya bayyana cewa ofishin ministan shari’a (AGF), hukumar NFIU, DSS da NIA na aiki wajen gano su, duk da cewa matsalolin shari’a na jinkirta bayyana sunayen wadanda ke daukar nauyin ta’addanci.
An gano wasu da ke da alaka da kasashen waje wajen daukar nauyin ta’addanci. An riga an kama wasu, an fara gurfanar da su, ciki har da wadanda suka kai hari a Owo. Amma tsarin shari’armu yana bata lokaci wajen yanke hukunci. Muna bukatar dokoki masu tsauri da kotunan musamman domin shari’ar ta’addanci,” in ji shi