Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPCL) ya bayyana cewa ya tafka asara mai yawa a watan Yuli, inda ribar da ya samu ta sauka daga Naira biliyan 905 a watan Yuni zuwa Naira biliyan 185 kacal. Wannan na nuna ragin kaso 79.6% cikin wata guda.
Rahoton wata-wata na kamfanin ya nuna cewa jimillar cinikin da NNPC ya yi a watan Yuli ya kai Naira tiriliyan 4.41, sabanin tiriliyan 4.57 da ya samu a watan da ya gabace shi.
Duk da cewa adadin danyen man da ake hakowa ya karu daga ganga miliyan 1.68 a kullum zuwa ganga miliyan 1.7, hakan bai hana ragin kudaden shiga ba.
NNPCL ya kuma bayyana cewa a watannin baya, ribar da ya samu ta kai Naira tiriliyan 1.05 a Mayu da biliyan 962 a Afrilu.