Mun samar da tsaro a Najeriya fiye da shekarun baya–Christopher Musa

0
6

Shugaban Rundunar Tsaron Ƙasa Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa kasar ta samu ingantuwar tsaro a yau fiye da yadda take shekaru biyu da suka gabata.

Ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels Television, ranar Alhamis, inda ya ce raguwar hare-hare da dawowar al’ummomi da dama zuwa rayuwarsu ta yau da kullum, na nuna ci gaban da aka samu a sha’anin tsaro.

“Ina ganin muna yin nasara. Na yi yawo a kasar nan, kuma ko’ina na je mutane suna yabawa da kokarin da muke yi,” in ji shi yayin da aka tambaye shi ko Najeriya ta fi zama lafiya yanzu.

Sai dai ya bayyana cewa har yanzu akwai hare-hare a wasu wurare, amma yawan faruwar su ya ragu matuka idan aka kwatanta da shekarun baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here