Gwamnatin tarayya, jihohi da kuma kananan hukumomi sun raba jimillar kuɗi naira tiriliyan 2.001 daga kudaden shiga na asusun tarayya na watan Yuli, 2025.
Wannan shi ne karo na farko da kudaden shiga suka kai wannan matsayi, bayan taron kwamitin raba kudaden shiga na FAAC da aka gudanar a Abuja a watan Agusta, 2025.
Sanarwar da kwamitin FAAC ya fitar ta nuna cewa daga cikin kudaden da aka raba akwai naira tiriliyan 1.282 a matsayin kudaden harajin da aka tattara, naira biliyan 640.610 daga kudaden VAT, naira biliyan 37.601 daga harajin canja kudi na intanet (EMTL), da kuma harajin musayar kuɗin kasashen waje na naira biliyan 39.745.
Jimillar kudaden da aka samu gaba daya a watan Yuli, 2025, ya kai naira tiriliyan 3.836, inda aka cire naira biliyan 152.681 a matsayin kudin tattara kudaden shiga, sannan aka ware naira tiriliyan 1.683 a matsayin kudaden ajiyar gwamnati da wasu fannoni na tallafi.