Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya taya matashin nan ɗan Jihar sa, Gwani Sanusi Bukhari Idris, murnar lashe matsayi na uku a gasar karatun Al-Qur’ani ta duniya da aka gudanar a kasar Saudiyya.
Yusuf ya bayyana cewa wannan nasara ba ta tsaya ga matashin da iyalansa kadai ba, illa ma dai babban alfahari ce ga jihar Kano, Najeriya, da dukkanin al’ummar Musulmi.
A cewarsa, wannan nasara ta kara tabbatar da irin gagarumin ci gaban da Kano ke da shi wajen samar da kwararru a ilimin Al-Qur’ani da tafsiri.
Gwani Sanusi Bukhari Idris ya wakilci Najeriya ne a gasar, inda ya samu nasara a rukunin Qira’at da Tafsiri.
Idan za a iya tunawa, a watan Disambar 2024, Gwani Sanusi Bukhari ya zama gwarzon gasar karatun Al-Qur’ani ta kasa karo na 39 da aka gudanar a jihar Kebbi.