Hukumar da ke yaƙi cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC) ta bayyana neman Abdullahi Bashir Haske, ɗan kasuwa a fannin man fetur kuma suruki ga tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ruwa-a-jallo.
Sanarwar da EFCC ta wallafa a shafukanta na sada zumunta ranar Alhamis da maraice, ta ce ana neman Haske ne bisa zargin halatta kuɗin haram da kuma haɗa baki wajen aikata wasu laifuka.
Shugaban sashen hulɗa da jama’a na hukumar, Dele Oyewale, wanda ya sanya hannu a kan sanarwar, ya bayyana cewa Haske, mai shekara 38, yana zaune ne a gida mai lamba 6 a titin Mosley, Ikoyi, Legas.
Har yanzu dai ba a samu jin ta bakin Haske ba kan batun.