Zamu ƙwato filayen da wasu mutane ke handame wa gwamnatin tarayya–Ministan Gida

0
10

Ministan gidaje da raya birane Ahmed Musa Dangiwa, ya bayyana cewar ma’aikatar sa zata haɗa hannu da rundunar ƴan sandan ƙasa don kwato kadarorin da wasu ɗaiɗaikun ƴan Najeriya ke yin rub da ciki akai duk da cewa arzikin ƙasa ne ba mallakin mutum guda ba.

Ministan ya bayyana hakan ne yayi da yayi wata ganawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja, lokacin da ya ziyarci sufeton yan sanda ƙasa Kayode Egbetokun.

Yace sau da dama ana samun wasu mutane ko kamfanonin dake mallakawa kansu kadarorin gwamnatin tarayya musamman filaye da sauran su a jihohi daban daban.

A cewar sa gwamnatin shugaba Tinubu, ba zata lamunci wannan dabi’a ba, saboda albarkatun kasa na kowa ne wanda ya kamata ayi amfani dasu ta hanyar da duk dan Najeriya zai amfana dasu.

Nan bada jimawa ba, zamu kafa wani kwamiti na haɗin gwiwa da rundunar ƴan sanda don taimakawa a kwato kadarorin gwamnatin da wasu mutane suka mallakawa kansu, da kuma mayar da filayen zuwa hannun gwamnati, inji ministan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here