Yawan masallatan da aka kashe a harin Katsina ya kai 32

0
7

Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da cewa adadin mutanen da suka rasa rayukansu a harin da ‘yan bindiga suka kai a masallacin Unguwan Mantau, karamar hukumar Malumfashi, ya kai mutum 32.

Harin ya faru ne da safiyar Talata, lokacin da jama’a ke cikin sallar Asuba. Maharan sun bude wuta kan masu ibada, lamarin da hukumomi suka bayyana a matsayin ramuwar gayya, bayan da al’ummar Ruwan Sanyi suka yi wa ‘yan bindiga kwanton-bauna kwanaki kadan da suka gabata, inda suka kashe da dama, suka kwato makamai da babura tare da ceto fursunoni.

A baya rahotanni sun ce mutum 13 ne suka mutu, amma a ziyarar ta’aziyya da tawagar gwamnatin jiha ta kai, aka tabbatar cewa 32 sun rasu, yayin da wasu kuma aka yi garkuwa da su.

Wasu daga cikin wadanda aka sace an ceto su bayan farmakin sama da sojojin sama suka kai, wanda ya tarwatsa harin. Haka kuma an tura karin dakarun soja da ‘yan sanda domin bin sawun maharan.

Gwamna Dikko Umar Radda, wanda yake hutun jinya, ya umurci mukaddashin gwamnan jiha, Malam Faruk Jobe, da ya tura tawaga mai girma karkashin jagorancin Sakataren Gwamnati, Abdullahi Faskari, domin jajanta wa iyalan mamatan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here