Shugaban NNPC ya karyata jita-jitar cewa matatun mai ba za su dawo aiki ba
Shugaban kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC), Bashir Bayo Ojulari, ya ce babu gaskiya a jita-jitar da ake yadawa cewa matatun mai na Warri, Fatakwal da Kaduna ba za su sake komawa bakin aiki ba.
Ojulari ya bayyana hakan ne a Abuja, yayin wani taron makamashi da ƙungiyar PENGASSAN ta shirya.
Ya jaddada cewa NNPC na É—aukar matakai masu muhimmanci domin tabbatar da cewa matatun za su dawo aiki yadda ya kamata nan bada jimawa ba.
Wannan martanin na NNPC na zuwa ne bayan kalaman mamallakin matatar Dangote, Alhaji Aliko Dangote, wanda ya yi ikirarin cewa ba lallai ne matatun gwamnatin tarayya su iya dawowa cikin aiki yadda ake fata ba.