Hisbah a Kano za ta ɗauki nauyin aurar da tubabbun ‘yan daba
Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta sanar da wani shiri na musamman domin ɗaukar nauyin aurar da matasa da suka tuba daga ayyukan daba.
Kwamandan rundunar Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana hakan ne yayin da sama da matasa 1,000 suka ajiye makaman su, suka kuma yi alƙawarin rungumar zaman lafiya.
A cewarsa, wannan shiri wani ɓangare ne na manufofin Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da ke nufin inganta rayuwar matasa da kuma ba su wata sabuwar dama ta ci gaba da rayuwa mai kyau.
Sheikh Daurawa ya ja kunnen matasan da suka tuba da su tsare mutuncinsu tare da zama nagari a cikin al’umma. Haka kuma ya yi kira ga sauran da ke cikin irin wannan dabi’a da su yi koyi da abokan su wajen barin laifi domin su ma su more zaman lafiya.
Wannan taro ya gudana ne a hedikwatar ‘yan sanda da ke Bompai, Kano, tare da halartar jami’an tsaro da shugabannin al’umma.