Gobara ta yi ɓarna a kasuwar dabbobi ta jihar Kwara

0
17

Akalla shaguna 22 sun ƙone kurmus a wata mummunan gobara da ta tashi a kasuwar dabbobi da ke Ajase-Ipo, karamar hukumar Irepodun, jihar Kwara, da misalin ƙarfe 1:35 na safe a ranar Laraba.

Rahotanni sun bayyana cewa gobarar ta samo asali ne daga wutar girki da wani daga cikin masu shagunan da bai kashe da kyau ba, wadda daga bisani ta bazu zuwa sauran shaguna.

Jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kwara, Hassan Hakeem Adekunle, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an yi nasarar dakile gobarar kafin ta kai sashen da ake ajiye dabbobi.

Daga cikin shaguna 323 da ke kasuwar, an tabbatar cewa an ƙonewar shaguna 22 na katako da kuma akwatunan kaya guda 6. Shagunan da abin ya shafa sun fi sayar da kayan abinci irin su shinkafa, gero, dawa, fulawa da kuma kayan masarufi.

Ya shawarci ‘yan kasuwa da mazauna gari da su kasance masu kula da matakan kariya daga gobara, musamman a kasuwanni da ake da tarin kayan da ke iya janyo gobara cikin sauƙi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here