Hukumar EFCC ta saki wasu manyan jami’ai biyu na Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) bayan sun mayar da kuɗaɗen da ake zargin sun karkatar daga hukumar.
Majiyoyi daga cikin hukumar sun bayyana cewa, yayin da jami’an biyu suka samu ’yancin kansu, akwai wasu manyan jami’ai guda shida da har yanzu ke hannun EFCC saboda sun ƙi mayar da kuɗaɗen da ake zargi sun yi amfani da su ba bisa ka’ida ba.
A baya-bayan nan, hukumar ta kama akalla manyan jami’ai guda takwas na NAHCON bisa zargin karkatar da kuɗaɗen da aka ware don gudanar da aikin Hajjin bana (2025).
Wannan bincike ya biyo bayan makamancin sa da ya faru a watan Agustan 2024, lokacin da tsohon shugaban NAHCON, Jalal Arabi, da sakatare Abdullahi Kontagora, suka shiga hannun EFCC bisa zargin yin amfani da tallafin kuɗin Hajji Naira biliyan 90 ba bisa doka ba. Daga bisani Shugaba Bola Tinubu ya tsige Arabi daga mukaminsa saboda lamarin.
Sai dai har yanzu EFCC ba ta fitar da cikakken jawabi kan sakamakon binciken da ake yi a halin yanzu ba.