Wani jigo a jam’iyyar APC, Dominic Alancha, ya yi gargadin cewa yiwuwar hadin gwiwa tsakanin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, da tsohon Gwamnan Anambra, Peter Obi, na iya zama barazana ga nasarar jam’iyyar mai mulki a zaben 2027.
Alancha ya bayyana hakan ne a wani shirin tattaunawa da Channels TV, inda ya ce idan Atiku da Obi suka haɗa kai za su iya tara ƙuri’u sama da miliyan 13 zuwa 14 abin da zai rage ƙarfin APC.
A watan Yuli, 2025, manyan ‘yan adawa ciki har da Atiku, Obi, Rotimi Amaechi, Nasir El-Rufai da David Mark sun rungumi jam’iyyar ADC a matsayin dandalin haɗin kai domin kalubalantar Shugaba Bola Tinubu.
Alancha ya kuma shawarci Tinubu da ya guji sake tsayawa da tsarin musulmi-musulmi kamar yadda aka yi a 2023, yana mai cewa hakan na iya sa jam’iyyar ta rasa goyon baya daga wasu sassan ƙasa.
Haka kuma, jigon na APC ya yi nuni da rade-radin yiwuwar dawowar tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan cikin siyasa, yana mai cewa akwai wasu daga Arewa da ke ƙoƙarin tura shi gaba don takarar 2027.
“Idan Jonathan, Atiku da Obi duk sun fito, tsarin musulmi-musulmi ba zai yi tasiri ba,” in ji shi.