Sojoji ba zasu iya magance rashin tsaron arewa ba–Gwamnan Kaduna

0
1

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa yaƙin sojoji da sauran hukumomin tsaro kaɗai ba zai wadatar wajen kawo ƙarshen ta’addanci da ƙungiyoyin masu tayar da kayar baya a Arewacin Najeriya ba.

Yayin wani taron ƙoli na jihohin Arewa maso Yamma da aka gudanar a Kaduna kan rige tsattsauran ra’ayi, gwamnan wanda kwamishinan tsaro na cikin gida, Sule Shuaibu, ya wakilta ya ce tushen matsalar rashin tsaro ya samo asali ne daga talauci, rashin adalci, cin hanci, rashin shugabanci nagari da kuma rashin damar samun aiki ga matasa.

Sani ya jaddada cewa har sai an magance waɗannan dalilai, nasarorin soji za su kasance. Ya yi kira da a ɗauki matakan haɗin gwiwa, haɗa kan al’umma, girmama haƙƙin ɗan adam da tabbatar da adalci wajen yaki da ta’addanci.

Shugaban Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Ƙasa (NCTC), Adamu Laka, ya goyi bayan wannan ra’ayi, inda ya ce ana bukatar tsari na al’umma da ya dogara da bayanan sirri wajen magance matsalar.

Rahotanni sun nuna cewa a cikin shekaru biyu da Gwamna Sani ya shafe a kan mulki, mutane 485 aka kashe yayin da sama da 1,700 aka yi garkuwa da su a Kaduna. 

LEAVE A REPLY

Logged in as Ismail Ishaq-Ibrahim. Log out?

Please enter your comment!