Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ta karyata rahotannin da ke cewa babu marasa lafiya daga arewa maso yamma cikin waɗanda za su ci gajiyar shirin rage farashin wankin ƙoda da gwamnati ta ƙaddamar.
A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, ma’aikatar ta ce labarin ba shi da tushe. Ta bayyana cewa shirin ya shafi dukkan ‘yan Najeriya, ba tare da wariya ba.
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ne ya amince da rage farashin wankin ƙoda daga Naira 50,000 zuwa Naira 12,000 a manyan asibitocin tarayya, karkashin shirin Renewed Hope na inganta rayuwar al’umma.
An fara aiwatar da shirin ne a asibitoci 11 da suka haɗa da Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, Asibitin Jami’ar Maiduguri, Asibitin Abubakar Tafawa Balewa a Bauchi, Asibitin Jami’ar Jos, Babban Asibitin Ƙasa na Abuja da wasu.
Ma’aikatar ta ce za a faɗaɗa shirin zuwa ƙarin asibitocin tarayya a faɗin ƙasar, tare da tabbatar da cewa babu wani ɗan Najeriya da za a bari a baya.