Gwamnatin Jihar Kano ta kafa wani kwamiti na musamman domin wayar da kan jama’a da karfafa halartar ‘yan kasa zuwa ga yin rijistar masu kada kuri’a da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta kaddamar a fadin Najeriya.
Kwamiti da aka kira zai kasance karkashin jagorancin Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, inda Sakataren Gwamnati na Jihar zai kaddamar da shi a hukumance.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun ofishin sakataren Gwamnatin Kano, Musa Tanko Muhammad, ya fitar ranar Talata, an bayyana cewa wannan mataki ba kawai shiri bane na gwamnati, illa dai wani muhimmin tsari ne domin tabbatar da cewa dukkanin ‘yan asalin jihar da suka cancanci rijista sun yi ta akan lokaci domin su samu damar kada kuri’arsu a zabuka masu zuwa.
Kwamiti ya kunshi wakilai daga manyan ma’aikatu, hukumomi, kwamitoci na gwamnati, kungiyoyin siyasa, kungiyar kwadago, dalibai, matasa, mata, masu sana’o’i da kungiyoyin farar hula.
Gwamnatin jihar ta jaddada cewa wannan kwamiti ba kawai na aikin ofishi bane, illa kuwa wani mataki na tabbatar da dimokuradiyya ta hanyar karfafa jama’a wajen shiga cikin harkokin zabe.
“Rijistar masu kada kuri’a ba al’ada ce kawai ba, hakki ne na dan kasa kuma shi ne hanya mafi muhimmanci da zai baiwa al’ummar Kano damar bayyana ra’ayinsu a akwatin zabe,” in ji sanarwar.