Gwamnatin Kano Ta Kaddamar da Kotunan Tafi-da-gidanka Don Hukunta Masu Keta Dokar Hanya

0
6

Hukumar Kula da Zirga-zirga ta Jihar Kano (KAROTA) ta kaddamar da kotunan tafi-da-gidanka domin hukunta direbobi da masu tukin adaidaita sahu da ke karya dokar fitilar bayar da hannu ga masu ababen hawa a cikin birnin Kano.

An kaddamar da shirin ne a ranar Talata, bisa umarnin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ƙara tsaurara bin doka da tabbatar da tsaron hanyoyi.

Shugaban KAROTA, Faisal Mahmud Kabir, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta saka sabbin fitilun bayar da hannu masu amfani da hasken rana a wurare daban-daban, inda ya yi kira ga jama’a su mutunta dokokin hanya.

Ya ce kotunan za su yi shari’a nan take ga masu laifi, domin tabbatar da kiyaye rayuka, kare dukiyoyi da kuma samar da ingantacciyar zirga-zirga a babban birnin jihar.

Haka kuma, Hukumar kiyaye afkuwar haɗura ta ƙasa FRSC reshen Kano ta bayyana shirinta na haɗa kai da KAROTA wajen tabbatar da nasarar wannan tsari, tare da kamawa da gurfanar da masu karya doka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here