Dokokin Tinubu basu yi amfani ba, a cikin shekaru 2–Legis360

0
9
Tinubu
Tinubu

Wani rahoto na Legis360 ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan dokoki 40 a cikin shekaru biyu na farko a mulkinsa, wanda ya ninka yawan dokokin da tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da su a sau uku, domin shi Buhari ya amince da dokoki 14 kacal daga 2015 zuwa 2017.

Sai dai rahoton ya nuna cewa duk da yawan dokokin da aka amince da su, hakan bai kai ga sanyawa ana ganin manyan canje-canjen gudanarwa ba.

Shugaban aikin Legis360, Samuel Folorunsho, ya ce manufar rahoton ita ce nuna yadda ake tafiyar da dokoki tsakanin majalisa da fadar shugaban kasa, tare da samar wa kungiyoyin farar hula da ‘yan jarida bayanai da za su taimaka musu wajen sa ido da tambayar gwamnati akan rawar da dokoki ke takawa wajen inganta rayuwar jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here