China ta ƙera saƙago da zai iya ɗaukar cikin haihuwa 

0
15

Kasar China ta kera saƙago wanda zai iya daukar ciki ta hanyar mahaifar na’ura.

 Wannan ci gaban kimiyya, wanda kamfanin Kaiwa Technology na Guangzhou ke jagoranta, zai fara aiki a shekarar 2026, kamar yadda rahoton Indian Times ya nuna.

Shugaban aikin, Zhang Qifeng, ya bayyana a taron ƙarawa juna sani na duniya akan saƙago, da aka gudanar a Beijing cewa matakin farko ya kammala, yanzu kuma ana kan shirin hade mahaifar ta na’ura da saƙagon domin samar da cikin.

A baya an taba amfani da irin wannan fasaha wajen tsare lafiyar dabbobi a Amurka a 2017. Amma sabuwar fasahar ta China za ta iya tafiyar da tsarin haihuwa daga haduwar maniyyi har zuwa haihuwa.

Ana sa ran farashin wannan sabuwar fasahar zai kasance kusan yuan 100,000 (kimanin £11,000). Masana sun ce hakan na iya zama mafita ga matsalar rashin haihuwa da ke karuwa a kasar China.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here