Amurka ta nuna damuwa kan tsaro da rashin adalci a Najeriya

0
8

Gwamnatin Amurka ta fitar da rahoton ta na Hakkokin Dan Adam na 2024, inda ta bayyana damuwa kan yadda ake gudanar da harkokin tsaro da shari’a a Najeriya. Rahoton ya ce akwai matsalolin bacewar mutane ba tare da dalili ba, tsare-tsare na tilas, da kuma jinkirin shari’u, musamman wadanda ake tsare da su kafin fara kammala shari’a.

A cewar rahoton, wasu mutane na cigaba da zama a kurkuku tsawon lokaci fiye da hukuncin da ake iya yanke musu idan aka kammala shari’arsu. Haka kuma, rashin isassun alkalai, cin hanci da rashawa, da tasirin siyasa suna kara jinkirta shari’u.

Game da tattalin arziki, rahoton ya ce sabon albashin ƙasa na Naira 70,000 bashi da ma’ana, saboda faduwar darajar naira, wanda yanzu ke kaiwa fiye da Naira 1,500 kan kowace dala. An kuma nuna cewa mafi yawan ma’aikata a Najeriya suna cikin tattalin arziki mara kyau , sannan doka ba ta iya kare su daga cin zarafi.

Sai dai Fadar Shugaban Kasa ta mayar da martani, inda ta ce gwamnati na aiki wajen gyara tsarin shari’a da kuma inganta harkokin tsaro. Kakakin Shugaba Tinubu, Sunday Dare, ya ce ana samun sauyi a tsaro.

Ya kuma bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya na samun daidaito, naira ta fara daidaita, kuma manufofin gwamnati na sake fasalin tattalin arziki na haifar da sakamako mai kyau.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here