Yan bindiga sun kai hari a Unguwan Mantau, dake karamar hukumar Malumfashi a jihar Katsina inda suka kashe mutum 13 a cikin masallaci yayin suke tsaka da yin sallar Asuba.
Kwamishinan tsaro na cikin gida, Dr. Nasir Mu’azu, ya bayyana cewa harin ramuwar gayya ne bayan al’ummar yankin sun kai wa ƴan bindiga farmaki kwanaki biyu da suka gabata, inda suka kashe da dama daga cikinsu tare da ceto mutane da aka yi garkuwa da su.
Gwamnatin jihar ta tura karin jami’an tsaro don dawo da zaman lafiya, tare da alkawarin kamo masu laifin da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.
Haka kuma, gwamnati ta yi ta’aziyya ga iyalan da abin ya shafa, tare da yabawa jarumtar al’ummar yankin wajen fuskantar ƴan ta’adda.