Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya amince da rage kudin wankin ƙoda daga Naira 50,000 zuwa Naira 12,000 a manyan asibitocin tarayya.
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsare-tsaren gwamnati, Daniel Bwala, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X, inda ya ce wannan mataki zai taimaka wa dubban marasa lafiya masu fama da cutar ƙoda.
An fara aiwatar da saukin kudin ne a asibitoci kamar su FMC Ebute-Metta (Lagos), FMC Jabi (Abuja), UCH Ibadan, FMC Owerri, da UMTH Maiduguri, kuma ana sa ran ƙara wasu asibitoci kafin ƙarshen shekara domin marasa lafiya a duk faɗin ƙasar su amfana.
A baya, Shugaba Tinubu ya amince da haihuwa ta hanyar tiyata kyauta a asibitocin gwamnati domin inganta lafiyar mata da kuma rage mace-macen da ake iya kaucewa.