Tinubu ya cire Kano da wasu jihohi daga tallafin wankin ƙoda

0
84

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya amince da rage kuɗin wankin ƙoda daga Naira 50,000 zuwa Naira 12,000 a manyan asibitocin tarayya a fadin ƙasar.

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan bayanai, Daniel Bwala, ya bayyana cewa wannan sauƙi zai taimaka wa dubban marasa lafiya da ke fama da cututtukan ƙoda.

Sai dai asibitocin tarayya da ke jihohin Arewa maso Yamma Kano, Kaduna, Jigawa, Katsina, Zamfara, Sokoto da Kebbi babu su a cikin jerin asibitocin da za a fara aiwatar da tallafin.

Rahotanni sun nuna cewa Jigawa na daga cikin jihohin da ke da yawan masu fama da cutar ƙoda a Najeriya.

Daga cikin asibitocin da aka fara aiwatar da wannan rangwame sun haɗa da, FMC Ebute-Metta (Lagos), FMC Jabi (Abuja), UCH Ibadan, FMC Owerri, UMTH Maiduguri, LUTH Lagos, FMC Abeokuta, FMC Azare, UBTH Benin, da UCTH Calabar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here