Tashin Bam ya kashe ƙananun yara a jihar Borno

0
9

An tabbatar da mutuwar yara biyu tare da jikkatar wasu guda shida sakamakon tashin bam a yankin Ƙofa Biyu, a Ƙaramar Hukumar Konduga ta Jihar Borno.

Shaidu a garin sun bayyana cewa yaran sun tono bam ɗin daga ƙasa suka ɗauko shi zuwa gida ba tare da sanin hatsarinsa ba, bisa tsammanin ƙarfe ne da za su sayar.

Mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 5 na yamma a ranar Lahadi. A cewarsa, bam ɗin ya fashe ne a hannun yaran, wanda ya yi sanadin mutuwar ɗaya daga cikinsu nan take, sannan ya jikkata wasu guda shida.

Daso ya ƙara da cewa ’yan sanda sun gaggauta kai waɗanda suka jikkata Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri, inda ake ci gaba da basu kulawa.

Ya kuma bayyana cewa rundunar tana ƙara wayar da kan jama’a kan illar tattara ƙarfe domin gujewa irin wannan hatsari, yana mai cewa makamancin haka ya taɓa faruwa a Konduga, Dikwa, Monguno da Jere duk da dokar hana tattara ƙarfe a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here