Rundunar ƴan sandan Kano zata hukunta jami’an ta akan rabon kuɗi

0
10

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta tabbatar da cewa tana daukar matakan ladabtarwa kan wasu jami’anta da aka gani a wani bidiyo da ya yadu suna taimaka wa wani ɗan siyasa wajen rabon kuɗi ga jama’a.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa bincike ya tabbatar da lamarin ya faru ne a ranar 10 ga Yuli, 2025 a fadar gwamnatin jihar Kano, bayan wani biki, ba kuma shi da alaka da zaɓen raba gardama da aka gudanar a ranar 16 ga Agusta, 2025 ba.

Ya ce jami’an da aka tura wajen tsaron wurin ne aka gani suna aikata abin da bai dace ba, kuma yanzu haka suna fuskantar ladabtarwa domin kare martabar rundunar.

Rundunar ta jaddada cewa za ta ci gaba da tabbatar da bin ƙa’ida da ɗa’a tare da tabbatar da amincin jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here