Rahotanni daga garin Gaya na Jamhuriyar Nijar sun bayyana cewa mata biyu sun rasa rayukansu bayan sun sha maganin ƙara kiba fiye da kima.
Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake dab da gudanar da gasar sarauniyar kiba da ake yi duk shekara a birnin Gaya.
An bayyana cewa suma waɗanda suka rasu ɗin sun sha wannan magani da manufar yin ƙibar da ta wuce misali don samun nasara a wannan gasa.