Kwankwaso ba zai haɗa kai da Tinubu ba, saboda rikicin masarautar Kano–Galadima

0
7

Babban jigon jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya bayyana cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa Rabiu Musa Kwankwaso ba zai yi goyi bayan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC ba a zaben 2027 mai zuwa.

Galadima ya yi wannan bayani ne a shirin Politics Today na Channels TV, inda ya ce gwamnatin Tinubu ta nuna wa Kwankwaso da jam’iyyarsa rashin adalci. Ya kuma zargi fadar shugaban ƙasa da mara Sarkin Kano na 15 Aminu Ado-Bayero baya a kan Muhammadu Sanusi II da aka dawo da shi sarautar Kano.

A cewar Galadima, abin da ake yi a Kano na naɗa sarakuna biyu a gari ɗaya ba daidai ba ne, tare da jaddada cewa gwamnati ta kasa kare rayukan al’umma yayin da jami’an tsaro ke takaita kansu wajen tsaron Aminu Ado-Bayero.

Ya ce wannan al’amari ya nuna cewa ba za a iya ganin Kwankwaso da APC a sahu ɗaya ba, kana ya tabbatar da cewa NNPP za ta taka muhimmiyar rawa a siyasar Najeriya musamman a babban zaben 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here