Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bada umarnin dakatar da da wasu asusun ajiyar kuɗi na bankin Jaiz, guda hudu da ake dangantawa da tsohon Shugaban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), Mele Kyari, bisa zargin almundahana.
Mai shari’a Emeka Nwite ya bada wannan umarni ne bayan lauyan hukumar EFCC, Ogechi Ujam, ya shigar da bukatar wucin gadi domin bada damar kammala bincike kan zargin almundahanar.
A cewar EFCC, an gano cewa fiye da Naira 661 miliyan ne ke ajiye a cikin asusun, kuma ana zargin kudaden na da nasaba da rashawa, cin hanci, da kuma amfani da kungiyoyi masu zaman kansu da taron ƙaddamar da littafi a matsayin wanda aka aikata ba daidai ba dasu.
Binciken ya kuma gano cewa Kyari ya yi amfani da iyalansa a matsayin wakilai wajen gudanar da asusun.
Kotun ta dage shari’ar zuwa ranar 23 ga Satumba, 2025, domin samun rahoton cigaban bincike daga EFCC.