Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin yaki da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta

0
7
Abba Gida-Gida
Abba Gida-Gida

Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da kwamitin mutane 18 domin dakile yawaitar yaran da ba sa halartar makaranta a fadin jihar.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kai na Ma’aikatar Ilimi, Balarabe Abdullahi Kiru, ya fitar a ranar Litinin, ya ce an kaddamar da kwamitin ne a ofishin Kwamishinan Ilimi, Dr. Ali Haruna Makoda. Wannan mataki na daga cikin kokarin gwamnati na samar da ilimi mai inganci da kuma shigar da kowane yaro a makaranta.

Dr. Makoda ya bayyana cewa shirin ya shafi yaran da ba su taɓa shiga makaranta ba, da kuma wadanda suka daina karatu. Ya ce an dora wa kwamitin nauyin faɗaɗa damar samun ilimi, inganta koyarwa da kuma samar da hanyoyin samun ƙwarewa da aikin yi nan gaba.

Kwamishinan ya kara da cewa kwamitin zai yi aiki wajen magance tushen matsalar ta hanyar rage talauci, da ƙarfafa shiga tsakani na al’umma, tare da samar da tsarin da zai magance matsalolin tsaro da ke hana yara zuwa makaranta.

A nasa jawabin, shugaban kwamitin wanda Umar Lawan ya wakilta, jagoran shirin Partnership for Learning for All in Nigeria Education (PLANE) da FCDO ke tallafawa, ya tabbatar da jajircewar kwamitin wajen aiwatar da ayyukansa yadda ya kamata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here