Gwamnatin Kano Ta Bai Wa Barau FC Damar Amfani Da Filin Sani Abacha

0
5

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kungiyar kwallon kafa ta Barau FC da ta yi amfani da filin wasan Sani Abacha da ke Kofar Mata a matsayin filin wasa na wucin gadi a gasar firimiyar Najeriya (NPFL) kakar 2025/2026.

Mataimakin Daraktan Yada Labarai na Barau FC, Ashiru Gidan Tudu, ya ce wannan mataki ya biyo bayan wata ganawa ta musamman tsakanin wakilan Hukumar Wasanni ta Jihar Kano da shugabannin kungiyar.

Asalin filin wasan Barau FC, wato Dambatta Stadium da ke Kano Arewa, yana cikin gyare-gyare a halin yanzu domin shiryawa sabuwar kakar wasa.

A wata sanarwa da ya fitar yau Talata, Shugaban Barau FC, Ibrahim Shitu Chanji, ya tabbatar da cewa an bai wa kungiyar izinin yin amfani da filin wasan Sani Abacha Stadium tsawon kakar gaba É—aya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here