Farfesa Haruna Musa, ya karɓi ragamar shugabancin jami’ar Bayero Kano, daga hannun Farfesa Sagir Adamu Abbas, wanda ya kammala wa’adinsa a matsayin shugaban jam’iyar na 11.
Sabon shugaban ya yi alkawarin gudanar da shugabanci na gaskiya da adalci, tare da bai wa hadin gwiwa da shawara muhimmanci domin ɗaukaka matsayin jami’ar zuwa matakin da za ta yi fice a duniya.
Ya kuma gode wa wanda ya gabace shi bisa jagoranci mai tasiri, tare da bayyana cewa zai ɗora akan ginshiƙan da tsoffin shugabannin jami’ar suka tafi don ci gaban jami’ar.