Yan sanda sun gurfanar da mutane 333 kan laifukan zabe a Kano

0
8

’Yan sanda sun gurfanar da mutane 333 kan laifukan zabe a Kano

Kwamishinan ’yan sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cewa rundunar ta gurfanar da mutane 333 a gaban kotun majistire dake Gyadi-Gyadi da kuma Nomansland, bisa zargin aikata laifuka yayin zaben cike gurbin da aka gudanar a kananan hukumomi Bagwai, Shanono, Tsanyawa da Ghari.

Bakori ya ce an kama mutanen ne da makamai irin su bindigogi, wukake da layoyi, tare da wasu kayayyakin zabe kamar akwatinan zuba kuri’a, takardun zabe (ballot papers) da kuma kudin da suka haura Naira miliyan 4.

Kwamishinan ya kuma bukaci al’ummar Kano da su ci gaba da bawa ’yan sanda hadin kai domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here