Wani mutum ya hana gina masallaci a unguwar Hausawa

0
1

Mazauna unguwar Hausawa da ke Kumbotso sun nemi daukin mahukunta kan zargin wani mutum mai suna Usman Ayya, da hana ginin masallacin unguwar.

Wasu daga cikin mazauna yankin, Ghali Rabiu da Surajo Iliyasu, sun ce mutumin yana kai su wajen jami’an tsaro don hana ci gaban aikin, duk da a cewar su ya tarar da su ne suna gina masallacin, kuma basu da wani wuri na gudanar da sallah a yanzu.

Wakilinmu ya tuntubi wani daga cikin ’yan uwan Usman, wato Alhaji Aminu Ayya, ta wayar salula amma bai amsa ba, haka kuma sakonnin da aka aika masa bai mayar da martani ba.

Dagacin Kumbotso, Aminu Iliyasu Kumbotso, ya tabbatar da korafin al’ummar yankin, inda ya ce Usman Ayya, ne ya tsaya kan hana aikin ginin masallacin, bisa dalilin cewa yana da niyyar saka lantarki mai amfani hasken rana a wurin.

LEAVE A REPLY

Logged in as Ismail Ishaq-Ibrahim. Log out?

Please enter your comment!