Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya mika sakon ta’aziyya ga shugaban jam’iyyar APC na yanzu, Dr. Nentawe Yilwatda, bisa rasuwar mahaifiyarsa, Lydia Yilwatda.
A cikin sakon ta’aziyyar da ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa, Edwin Olofu, Ganduje ya bayyana marigayiyar a matsayin mace mai tsoron Allah wadda ta yi rayuwa ta hidima ga Ubangiji, iyali da al’umma. Ya kara da cewa kyawawan dabi’unta da tarbiyya sun bayyana a jagorancin ɗanta wanda yanzu ke shugabantar jam’iyya mai mulki.
Ganduje ya ce rashin uwa na daga cikin manyan ciwo da rayuwa ke haifarwa, amma ya bukaci iyalan Yilwatda su yi hakuri da cewa Lydia, tayi rayuwa mai cike da kima, tausayi da tarbiyya.
“Ina mika sakon ta’aziyya daga gare ni, iyalina, abokaina da magoya bayana ga shugabanmu na kasa, Dr. Nentawe Yilwatda da iyalansa baki ɗaya. Mama Lydia za a ci gaba da tunawa da ita bisa kyawawan dabi’u, sadaukarwa da gudummawar da ta bayar ga al’umma.
Ya kuma yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar APC a fadin kasar nan da su nuna goyon baya da juriya ga shugaban jam’iyyar a wannan lokaci mai wahala.