Cutar mashaƙo ta kashe yara huɗu ƴan gida ɗaya a Kano

0
2
Kano

Cutar mashaƙo (diphtheria) tayi sanadiyar mutuwar yara huɗu yan gida ɗaya a unguwar Hotoron Yan Dodo, dake ƙaramar hukumar Tarauni a jihar Kano.

Rahotonni sun bayyana cewa lamarin ya faru a cikin makonni biyu.

Mahaifin yaran, Malam Yusuf Maitama, ya bayyana cewa ƙaddarar ta fara ne da ƙaramin ɗansa mai ƙasa da shekaru biyar, wanda ya fara fama da zazzaɓi da ciwon maƙogwaro kafin daga bisani ya rasu. Bayan haka kuwa, sauran uku daga cikin ‘ya’yansa suka nuna irin waɗannan alamomin, duk da ƙoƙarin ceto su, amma sun rasu, sai babbar ‘yarsa ce kaɗai ta tsira bayan an kai ta asibiti cikin gaggawa.

Rahotanni sun nuna cewa yaran sun nuna alamomin cutar ta mashaƙo irin su zazzaɓi mai zafi da ciwon maƙogwaro.

Bayan faruwar lamarin, jami’an lafiya sun kai ziyara gidan, inda suka tsaftace muhallin tare da yi wa sauran yara rigakafin cutar a unguwar, domin hana yaduwar ta.

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta ware asibiti na musamman domin kula da masu fama da cutar, tare da tabbatar da cewa ana bayar da rigakafi da magani kyauta ga dukkan yara. Haka kuma ta yi kira ga iyaye da su tabbatar da yin rigakafin yara da kuma gaggauta kai su asibiti idan aka fara samun alamomin cutar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here