An kama ɗan wanda ya kafa Boko Haram

0
18

Jami’an tsaron Chadi sun kama mutum shida da ake zargi da ta’addanci, ciki har da Muslim Mohammed Yusuf, ɗan marigayi Mohammed Yusuf, wanda ya kafa Boko Haram.

Rahotanni sun nuna cewa Muslim, mai shekaru 18, shi ne ya shugabanci wata  ƙungiya, wacce ta fito daga ISWAP bayan ballewa daga Boko Haram.

An ce yana amfani da sunan Abdrahman Mahamat Abdoulaye, kuma yana da ƙani mai suna Habib Yusuf (Abu Mus’ab Al-Barnawi), jagoran ISWAP.

Hotunan da suka bayyana sun nuna matashin cikin kayan motsa jiki na shuɗi tsaye tare da wasu tsofaffi da aka kama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here