Wani tsoho mai shekara 60 ya kamu da cutar da ba kasafai ake kamuwa da ita ba bayan ya yi amfani da shawarar AI.
Hakan ya sanya an kwantar da shi a asibiti bayan ya kamu da wata cuta mai wuya da ake kira bromism, sakamakon maye gurbin gishirin tebur da sodium bromide, bisa shawarar da ya samu daga ChatGPT.
Rahoton da aka wallafa a mujallar Annals of Internal Medicine Clinical Cases a ranar 5 ga Agusta, 2025, ya nuna cewa mutumin ya tambayi chatbot É—in madadin gishiri, inda aka ba shi shawarar amfani da bromide maimakon chloride. Na tsawon watanni uku yana siyan sodium bromide ta yanar gizo, yana kuma amfani da shi a matsayin gishirin cin abinci.
Bayan wani lokaci, likitoci sun ce ya fara fuskantar matsaloli irin su damuwa, ganin abubuwan da babu (hallucination), rashin barci, ƙishirwa sosai, rashin daidaiton motsi da matsalar fata, abin da ya sa aka kwantar da shi a sashen lafiya na kwakwalwa.
Gwaje-gwajen likita sun gano cewa bromide ya shafi sakamakon gwaje-gwaje na jini, wanda ya taimaka wajen gano cewa yana fama da bromism, cutar da aka daina ganin ta tun ƙarshen ƙarni na 20 bayan an cire bromide daga magunguna. Bayan kulawa da magungunan gyaran sinadaran jiki da kuma na kwakwalwa, an samu sauƙi a jikinsa bayan makonni.
Masana kiwon lafiya sun ja kunnen jama’a da cewa bai kamata a dogara kacokan da AI wajen samun shawarar lafiya ba. Sun jaddada cewa ko da yake chatbots na iya bayar da bayanai masu ma’ana, amma ba za su iya maye gurbin Æ™warewar likitoci ba. Don haka, shawarar likita ta musamman tana da matuÆ™ar muhimmanci a duk abin da ya shafi lafiya da abinci.