Ruwan sama mai ƙarfi ya mamaye garin Potiskum a Jihar Yobe, inda ambaliya ta lalata gidaje da dama tare da raba jama’a da muhallansu.
Ruwan saman da ya sauka a daren Juma’a ya rushe gidaje da dama, ya kuma tilasta wasu daga cikin mazauna komawa sansanonin ’yan gudun hijira, yayin da wasu suka nemi mafaka a wajen ’yan uwansu.
Wani mazaunin garin, Musa Adamu, ya shaida cewa, gidaje da yawa sun rushe amma babu wanda ya rasa ransa. Yawancin mutanen da abin ya shafa sun bar muhallansu saboda lalacewar gidajensu.”
Yankunan da suka fi fuskantar barna sun hada da Arikime, Ramin Kasa, Tandari, Nahuta, Boriya, Rugar Fulani, da Unguwar Kuwait.
Sauran wuraren da ambaliyar ta shafa sun haɗa da Old Prison, Filin Nashe, Unguwar Makafi/Majema, Unguwar Jaji Bakin Kwari, Afghanistan, Tsangaya Bakin Kwari, Karofi, Bayan Garejin Danjuma, da bayan Fudiyya Potiskum.