Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kuɗaɗen albashi da kudaden gudanar da ofisoshin Sanatoci 109 na Majalisar Dattawa, wanda ya kai kusan Naira biliyan 2.354 a wata, sun isa a biya albashin malaman jami’a 4,708 masu matsayi na Farfesa a fadin ƙasar nan.
Rahoton ya nuna cewa har yanzu ana ta muhawara kan yadda ake biyan manyan ‘yan siyasa albashi fiye da malaman jami’a.
Daily Trust ta ce Farfesa yana samun matsakaicin albashin kusan Naira 500,000 a wata, yayin da Sanata guda ke karɓar kusan Naira 21.6 miliyan.
A ranar 14 ga Agusta, 2024, Sanata Kawu Sumaila daga Kano ta Kudu ya shaida wa BBC Hausa cewa shi da kansa yana karɓar Naira 21.6 miliyan a kowane wata, ciki har da albashi da kuɗin gudanar da ofishi, abin da ya ce ya yi daidai da albashin Farfesoshi sama da 40.
Ya ƙara da cewa, albashin mu na ainihi bai kai miliyan ɗaya ba a wata, idan aka cire haraji da wasu kudade, yana raguwa kusan Naira 600,000. Amma kowanne Sanata yana samun Naira 21 miliyan a matsayin kuɗin gudanar da ofisinsa.