0
3

Ƴan ta’adda sun ɗana Bam a wata gona dake jihar Borno

Rundunar ‘Yan Sanda ta Borno ta tabbatar da ganowa da kuma lalata wani bam da bai fashe ba a wata gona da ke ƙaramar hukumar Dikwa.

Kakakin rundunar, ASP Nahum Daso, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin cewa wani manomi mai suna Babagana Kachalla ne ya gano Nam ɗin a cikin gonar sa, inda ya hanzarta kai rahoto ga jami’an tsaro.

Bayan rahoton, Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, Naziru Abdulmajid, ya tura kwararrun sashen lalata bama-bamai (EOD) daga Maiduguri zuwa wurin. Da suka isa, sun tabbatar da cewa abin da aka gano shi ne babban bam ɗin Cluster Bomb Unit (CBU) mai tsawon mita 2.2 da fadin santimita 30.

EOD-CBRN ta tarwatsa bam ɗin, sannan ta cire sassan bam ɗin ba tare da wani lahani ya faru ba.

Rundunar ta kuma yi amfani da wannan dama wajen wayar da kan al’umma game da haɗarin bama-bamai, tare da gargadin su kasance cikin faɗakarwa da kuma hanzarta sanar da jami’an tsaro idan sun ga wani abin da ake zargi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here