Zaben Cike Gurbi a Kano: NNPP da APC Sun Yi Nasara a Mazabu Daban-daban

0
13

A zaben cike gurbi da aka gudanar a Kano, jam’iyyun NNPP da APC sun samu nasara a wurare daban-daban.

A mazabar Bagwai/Shanono, jami’in zabe Farfesa Hassan Shitu ya bayyana Aliyu Kiyawa na NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 16,198, inda ya doke dan takarar APC da ya samu 5,347.

Sai dai a Ghari/Tsanyawa, jami’in zabe Farfesa Muhammad Waziri ya sanar da cewa Garba Gwarmai na APC ya yi nasara da kuri’u 31,472, ya doke NNPP wadda ta samu 27,931.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here