Shugaba Tinubu Ya Taya Babangida Murnar Cika Shekaru 84

0
10

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), murnar cika shekaru 84 a duniya.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya bayyana farin cikinsa tare da iyali, abokai da masoya na Janar Babangida, wanda ya ce mulkinsa na shekaru takwas ya taka rawar gani wajen ci gaban siyasa da tattalin arzikin ƙasa.

Shugaba Tinubu ya jinjina gagarumin tarihin aikin soja na Babangida, wanda ya haɗa da zama malami a NDA, kwamandan rundunar sojoji da kuma babban hafsan sojojin ƙasa.

Ya kuma ce Babangida ya yi manyan ayyuka, ciki har da gina gadar Third Mainland Bridge dake Lagos, kafa hukumomin tsaro kamar SSS, NIA, DIA da FRSC, tare da kirkirar jihohi da kuma mayar da babban birnin ƙasa daga Lagos zuwa Abuja.

Shugaban ƙasar ya gode masa bisa jajircewarsa da hidimar da ya bai wa ƙasa, tare da roƙon Allah ya ƙara masa lafiya da tsawon rai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here