NNPP Ta Yi Watsi da Sakamakon Zaɓen Ghari/Tsanyawa

0
15

Jam’iyyar NNPP ta ƙalubalanci sakamakon zaɓen cike gurbi na majalisar jiha a Ghari/Tsanyawa, tana mai zargin hukumar zaɓe INEC da APC da haɗa baki wajen yin maguɗi.

Shugaban NNPP na jiha, Hashimu Dungurawa, ya ce an gudanar da zaɓen cikin lumana, amma INEC ta soke sakamakon rumfunan da kotu ta umarta a sake zaɓe, ta kuma koma kan tsohon sakamakon da ake kalubalanta a kotu.

NNPP ta yi gargadin cewa ba za ta yarda da abin da ta kira rashin adalci da fifita jam’iyya ɗaya ba, duk da haka ta yaba da sahihancin zaɓen Shanono/Bagwai inda ɗan takararta ya yi nasara.

A sakamakon Ghari/Tsanyawa, INEC ta ayyana Garba Ya’u Gwarmai na APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ƙuri’u 31,472, inda ya doke Yusuf Ali Maigado na NNPP da ya samu ƙuri’u 27,931.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here