Jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya gode wa al’ummar Bagwai da Shanono bisa irin goyon bayan da suka nuna wa jam’iyyar a zaɓen cike gurbi da aka kammala.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Lahadi, Kwankwaso ya bayyana nasarar ɗan takarar NNPP, Ali Lawan Alhassan, a matsayin babbar nasara wadda ta nuna inda amincin jama’a ya ke yanzu da nan gaba.
Ya yaba wa shugabanni da magoya bayan jam’iyyar bisa jajircewa da kuma gudanar da zaɓen cikin lumana da tsarin dimokuraɗiyya.
Kwankwaso ya ce, “Mutanen Bagwai da Shanono sun bayyana ra’ayinsu ta hanyar ba da kuri’a mai tarin yawa ga jam’iyyarmu, wanda ya nuna amincin da suke da shi gare mu.”
Haka kuma ya sake jinjinawa ƙoƙarin ‘yan jam’iyyar da magoya baya da suka yi aiki tukuru wajen ganin zaɓen ya gudana cikin lumana tare da samun nasara.