Yan Sanda Sun Kama ƴan daba zasu tayar da tarzoma a zaɓen Ɓagwai da Shanono

0
14

Jami’an tsaro sun cafke wasu mutane da ake zargin suna shirin tayar da tarzoma a guraren zaɓen cike gurbi da ake gudanarwa a kananan hukumomin Shanono da Bagwai na Jihar Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa an kama su ne a wasu rumfunan zaɓe inda ake zargin suna ƙoƙarin tarwatsa masu kaɗan kuri’a.

Hukumomi dai ba su bayyana sunayen waɗanda aka kama ba, haka kuma ba su fayyace irin laifin da ake zargin su da shi ba.

Amma zuwa yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here