Masarautar Rano Ta Haramta Aurar Da Mata Kafin Su Kammala Firamare

0
10

Masarautar Rano ta jihar Kano ta fitar da umarni na haramta cire yarinya daga makaranta domin aurar da ita kafin ta kammala karatun firamare.

Wannan sanarwar ta fito ne daga sakataren yada labaran masarautar, Nasiru Habu Faragai, a ranar Jumu’a, inda ya ce Sarkin Rano, Ambasada Dakta Muhammad Isa Umaru, ya bayyana haka a lokacin bikin kaddamar da shigar sababbin ɗalibai aji ɗaya na shekarar 2025/2026 da aka gudanar a garin Lausu, cikin haɗin gwiwar SUBEB, UBEC da UNICEF.

Sarkin ya umarci dagatai, masu unguwanni, sarakunan Fulani da malamai da su tabbatar da bin wannan doka, tare da gargadin cewa duk wanda ya karya ta za a ɗauki matakin ladabtarwa a kansa.

Haka kuma, ya ja kunnen iyaye da malamai kan su guji hada baki wajen fitar da yarinya daga makaranta don aurar da ita, yana mai cewa hakan babban cikas ne ga ci gaban rayuwar yara mata.

A ƙarshe, Sarkin ya roƙi iyaye da shugabannin al’umma su bayar da haɗin kai da goyon baya ga gwamnati a ƙoƙarinta na inganta ilimi a jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here