Kotu ta bayar da umurnin a kamo  Dagacin Tamburawa

0
16

Kotun Shari’ar Musulunci da ke shelkwatar rundunar Hisbah a Kano, ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Malam Sani Tanimu Sani Hausawa, ta bayar da umarnin a kamo Dagacin garin Tamburawa, dake ƙaramar hukumar Dawakin Kudu, Alhaji Auwal Umar Dantube, bisa kin bayyana a gaban kotu.

An gurfanar da Dagacin tare da wani yaron sa, Sulaiman Dogo Matage, bayan iyalan marigayi Alhaji Mammada Tamburawa sun shigar da ƙorafi akan su a ofishin ‘yan sanda na Zone One, inda suka zarge su da bata suna, cin dukiya ba bisa ka’ida ba da kuma tayar da hankalin jama’a.

Sai dai da sanyin safiyar ranar zaman  shari’ar, lauyan da ke kare Dagacin, Barrister Tijjani Kabir Dukawa, ya kai shi kotu kafin ‘yan sanda su kamo shi. Bayan karanta masa tuhumar da ake yi masa, ya musanta laifin, inda lauyansa ya roƙi a bayar da shi a beli.

Mai shari’a ya amince da bayar da belin bisa sharuddan ya kawo mutane biyu masu tsaya masa, wanda zasu kasance ɗaya daga cikin iyalansa ko matarsa, ɗaya kuma daga mai unguwa ko wani dagaci a ƙarƙashin Hakimin Dawakin Kudu. Haka kuma dole ne wanda zai tsaya masa ya gabatar da takardar ɗaukar aiki daga gwamnati, da katin shaida na aiki.

Kotun ta bada umarnin a tsare shi har sai an cika waɗannan sharudda, sannan ta dage cigaban shari’ar zuwa ranar 28/08/2025 domin masu ƙara su gabatar da shaidu.

Bayan zaman kotun, ƙoƙarin jin ta bakin lauyan Dagacin ya ci tura. Sai dai ɗaya daga cikin marayun da suka shigar da ƙara ya shaida cewa suna roƙon kotu ta karɓo musu hakkinsu da suka ce dagacin ya cinye, domin a cewarsa Dagacin bai da wani ikon da zai tauye musu hakkinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here