Matatar Dangote ta Shirya Jigilar Man Fetur Kyauta ga Gidajen Mai

0
9
Aliko-Dangote
Aliko-Dangote

Matatar man Dangote ta sanar da fara jigilar mai kyauta kuma kai tsaye zuwa gidajen mai a faɗin Najeriya daga yau, wani mataki da ake ganin zai kawo babban sauyi a harkar man fetur a ƙasa.

Kamfanin ya bayyana cewa wannan tsarin zai rage yawan masu shiga tsakani, ya inganta tsarin rarraba mai, tare da bai wa gidajen mai da masu amfani dashi damar samun mai a farashi mai sauƙi.

Matatar man, wacce ke da ƙarfin tace ganga 650,000 a rana, ta fara aiki a shekarar 2023, inda ta taka muhimmiyar rawa wajen rage tsadar mai bayan tashin gwauron zabin da ya biyo bayan cire tallafin mai da Shugaba Bola Tinubu ya yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here